Darajar kayan da ake samarwa da ayyuka ya karu da kashi 6.7 cikin dari a shekarar 2016, bisa ga kiyasin gwamnati. A watanni ukun karfin karshen shekara, darajar ya kai kashi 7.1 cikin dari wanda ya haura duk na wata kasar Asia.Hukumar bada Lamuni ta kasa da kasa wato IMF ta kimanta tattalin arzikin Philippine yanzu ya kai dalolin Amurka biliyan 311.
Kakakin shugaban Philippine Ernesto Abella ya lissafto nasarorin da kasar ta samu daga huldarta da kasashen waje wandanda sune sanadiyyar bunkasar tattalin arzikin kasar. Tun a watan Yunin shekarar 2016, shugaba Rodrigo Duterte ya kulla sabuwar dangantaka da China tare da kuma kyautata dangantakarsu da Japan.