Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Rasha Ta Ce Ba Zata Kori Jami'an Amurka Ba


Ofishin jakadancin Amurka a birnin Moscow
Ofishin jakadancin Amurka a birnin Moscow

Kasar Rasha tace ba zata 'dauki matakin korar jami'an diflomasiyyar Amurka ba, a matsayin mayar da martani ga takunkumin da Amurka ta kakaba mata.

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya fadi a birnin Mascow cewa ba zai kori jami'an diflomasiyyar Amurka ba a matsayin martanin takunkumin da Shugaban Amurka Barack Obama ya kakaba jiya Alhamis saboda zargin cewa jami'an leken asirin Rasha sun yi katsalandan a babban zaben Amurka da aka yi a watan Nuwamba.

"Ba za a haddasa matsala ga jami'an diflomasiyyar Amurka ba. Ba za mu kori kowa ba," a cewar Putin a wani bayanin da fadar Kremlin ta fitar.

Gabanin nan, kafar labaran Rasha ta Interfax ta ruwaito Ministan Harkokion Waje Sergei Lavrov na cewa ya bayar da shawarar cewa Shugaba Putin ya kori jami'an diflomasiyyar Amurka 35 ya kuma hana iyalan jami'an diflomasiyyar Amurka amfani da gidajen hutu na ofishin jakadanci da ke yammacin birnin Mascow da kuma wani gidan ajiya da ke arewacin birnin.

Jiya Alhamis Obama ya mai da martani kan Rasha da wasu jerin matakan takunkumi, ta wajen kakaba takunkumi kan wasu cibiyoyin leken asiri biyu, ya sanar da korar jami'ai 35 ya kuma rufe wasu gine-ginen diflomasiyyar Rasha biyu a Amurka. Nan da nan Rasha ta yi Allah wadai da takunkumin da cewa baya bisa ka'ida sannan ta yi barazanar mai da martani.

XS
SM
MD
LG