Jimillar ‘yan sanda dake rasa rayukkansu a bakin aiki ya karu a wannan shekara mai karewa a nan Amurka, a sabili da hare-haren da ake ta kaiwa kan jami’an tsaro, kamar wadanda aka kai a biranen Dallas ta jihar Texas da Baton Rouge ta jihar Louisiana.
Wani sabon rahoton da Asusun Tunawa da ‘Yan sanda na Amurka ya fito da shi jiya yace ‘yan sanda 135 aka kashe a wannan shekara a nan Amurka yayinda suke bakin aiki.
Da yawansu sun mutu ne a cikin hatsurran mota, amma kusan rabinsu duk an harbe su ne da gangan, aka yi musu kisan gilla.
Wannan jimillar ta nuna cewa an sami karin kashi 56 cikin 100 fiye da wadanda aka rasa a shekarar da ta gabata.
Shugaban Asusun Tunawa da ‘Yan sandan, Craig Floyd, yace bai taba ganin shekarar da aka yi asaran ‘yan sanda da yawa kamar bana ba.