Tattalin Arzikin Najeriya Ya Bunkasa Da Kaso 3.46

Kayan abinci a kasuwar Najeriya

Sanarwar da babban jami’in kididdiga na tarayyar kasar, Adeyemi Adeniran Adedeji ya fitar, tace bunkasar ta dara wacce aka gani a zango na 3 na shekarar 2023 da ta gabata (ta kaso 2.54 cikin 100) da kaso 0.92 cikin 100.

Tattalin arzikin Najeriya ya bunkasa a zahiri da kaso 3. 46 cikin 100 a zango na 3 na shekarar 2024 da muke ciki a bisa kididdigar shekara zuwa wata, kamar yadda hukumar kididdigar Najeriya (NBS), ta bayyana.

Sanarwar da babban jami’in kididdiga na tarayyar kasar, Adeyemi Adeniran Adedeji ya fitar, tace bunkasar ta dara wacce aka gani a zango na 3 na shekarar 2023 da ta gabata (ta kaso 2.54 cikin 100) da kaso 0.92 cikin 100.

Sanarwar ta kara da cewa zangon ya dara wanda ya gabace shi (zango na 2) na 2024 da kaso 3.19 cikin 100.

“Hakan na nuna samun bunkasa idan aka kwatanta yadda al’amarin yake a irin wannan zango a shekarar da ta gabata (2023) da kuma na zangon da ya gabaci wannan din (zango na 2 na 2024).

Babban bangaren tattalin arzikin da ya fi ingiza bunkasar shi ne na ayyuka, wanda ya samu bunkasar kaso 5.19 cikin 100 kuma ya bada gudunmowar kaso 53.58 na jumlar bunkasar da aka samu.