Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kaso 2 Cikin 3 ‘Yan Najeriya Basu Da Kudin Sayen Lafiyayyen Abinci - NBS


Kayan abinci a kasuwar Najeriya
Kayan abinci a kasuwar Najeriya

Haka kuma binciken ya gano cewa iyalai a kasar na fuskantar kaso 6.7 na daukewar hasken lantarki a kowane mako.

Rashin kudi ya jefa kaso 2 cikin 3 na magidanta a Najeriya na cikin gararin kasa samar da lafiyayyen abinci mai gina jiki, a cewar binciken da hukumar kididdigar kasar (NBS) ta gudanar.

Binciken NBS din mai taken, “bincike a kan magidantan Najeriya, ya yi duba a kan matsanacin talaucin dake addabar kasar da kuma tasirin ci gaba raguwar damar ‘yan Najeriyar ta iya sayen kayan masarufin da suke bukata saboda matsalar hauhawar farashi.

Game da matsalar rashin wadatar abinci binciken ya bayyana cewa: “kusan kaso 2 cikin 3 na magidanta sun bayyana gazawarsu wajen iya cin lafiyayyen abinci mai gina jiki ko kuma irin wanda ransu ke so saboda rashin kudade a kwanaki 30 din da suka gabata.

Haka kuma, kaso 68.3 cikin 100 na magidantan na iya cin nau’uka kalilan ne na kayan abinci saboda kamfar kudade, sannan kaso 62.4 na damuwa a kan rashin wadatar abincin da za su ci, a yayin da kaso 60.5 cikin 100 ke cin kasa da kason abincin da ya kamata su ci.

Haka kuma binciken ya gano cewa iyalai a kasar na fuskantar kaso 6.7 na daukewar hasken lantarki a kowane mako.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG