Martin Kobler, Shugaban tawagar bada tallafi ta MDD a Libiya, ya gaya ma Kwamitin Tsaron MDD jiya Talata cewa yawan man fetur da kasar ke samarwa ya yi faduwar da bai taba yi ba, saboda a yanzu ta na samar da ganga 200,000 ne kadai a rana guda - wanda wannan babbar raguwa ce idan aka kwatanta da ganga wajen miliyan 1 da dubu 400 da ta ke samarwa bayan juyin juya halin 2011 da ya kai ga hambare tsohon shugaban kasar, Shugaba Moammar Gadhafi mai kama karya.
"A yanzu akwai gibin kashi 75% a kasafin kudin kasar ke nan," a cewar Kobler.
Libiya ta samu kanta cikin rudami da tashe-tashen hankulla masu nasaba da tarzomar cikin gida ta siyasa a tsakanin bangarorin mayaka a birnin Tripoli da kuma yammacin kasar, sannan kuma ga illar kwace yankunan kasa da kungiyar ISIS ta yi.
Kobler ya kuma ce kasar ta zama zango na karshe ga bakin haure masu kokarin kaiwa kasashen Turai, ta yadda sama da 100,000 su ka isa gabar Italiya a wannan shekarar kawai ma, daga wannan kasar ta Arewacin Afirka.
A gefe guda kuma, Kobler ya ce kwalliya ta biya kudin sabulu a farmakin da sojojin Libiya ke kai wa kan ISIS a birnin Sirte. "Kwanan nan, kungiyar ISIS za ta daina iko da ko da yanki guda a Libiya," a cewarsa.