Tattalin Arziki: Gwamnati Ta Baiwa ‘Yan Najeriya Tabbacin Cewa Al’amura Zasu Yi Kyau A Karshe

  • VOA Hausa

Abubakar Atiku Bagudu

A jawabinsa yayin karo na 30 na taron kolin Najeriya a kan tattalin arziki daya gudana a Abuja, Ministan Kasafi Da Tsare-Tsare, Atiku Bagudu, ya baiwa ‘yan Najeriya tabbacin cewa duk da halin matsin da ake fama da shi a kasar, akwai fatan samun sauki a nan gaba.

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta baiwa ‘yan Najeriya tabbacin cewa bayan wuya dadi na zuwa yayin da take bijiro da manufofi da nufin sake farfado da tattalin arzikin kasar.

Bayan hawa karagar mulki a bara, Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya bullo da sauye-sauye da nufin zaburar da tattalin arzikin Najeriya tare da janyo masu zuba jari daga ketare.

Sai dai, babu abin da ‘yan najeriya suka gani illa hauhawar farashin man fetur da kayan masarufi da ba’a ga irinsu ba a shekaru 30 da suka gabata tun bayan da tinubu ya janye tallafin man fetur da sakin naira babu kaidi.

A jawabinsa yayin karo na 30 na taron kolin Najeriya a kan tattalin arziki daya gudana a Abuja, Ministan Kasafi Da Tsare-Tsare, Atiku Bagudu, ya baiwa ‘yan Najeriya tabbacin cewa duk da halin matsin da ake fama da shi a kasar, akwai fatan samun sauki a nan gaba.

A cewa ministan, harkokin cinikayyar Najeriya na ketare sun inganta a zango na 2 na shekarar 2024 abin da ke alamanta cewa sauye-sauyen gwamnati mai ci na aiki.

Bagudu ya kuma bayyana kwarin gwiwa game da halin da tattalin arzikin Najeriya ke ciki, inda yace yana fuskantar alkiblar da ta dace a bisa ma’aunai daban-daban ciki har da raguwar hauhawar farashi.