Tattalin Arziki: An Bude Taron Gwamnonin Jihohin Yankin Tafkin Chadi

Taron Gwamnonin Tafkin Chad Da Matasa Don Zaman Lafiya

Gwamnan jihar Bornon Najeriya, Farfesa Baba Gana Umara Zulum, na daga cikin gwamnonin da ke wakiltar Najeriya a taron. Ya ce wajibi ne a tsara ayyukan raya karkara domin cimma burin da aka sa gaba.

A yau aka bude gwamnonin jihohin da ke yankin Tafkin Chadi a Jamhuriyar Nijar da nufin tantauna hanyoyin farfado da tattalin arzikin al’umomin da rikicin Boko Haram ya jefa cikin kangin rayuwa.

Taron wanda shi ne karo na biyu da hukumar raya Tafkin Chadi ke shiryawa, wata hanya ce da ke bai wa hukumomi da talakawan yankin damar hada hannu a tsakaninsu domin tsayar da magana daya a game da matsalolin da suka fi addabarsu bayan rikicin Boko Haram.

Sakataren zartarwar hukumar ta raya tafkin Chadi, Ambasada Nuhu Mamman, ya ce gwamnoni su ne suka fi kusa da mutane, wato mutanen da rikicin ya fi shafa, dalilin da ya sa aka hada wannan taron.

Samar da tsaro ta hanyar ayyukan farfado da tattalin arziki da abin da ya shafi makomar ‘yan gudun hijira, na daga cikin abubuwan da taron na birnin Yamai zai maida hankali akansu inji Gwamnan Diffa Mohamed Moudour.

Gwamnan jihar Borno Farfesa Baba Gana Umara Zulum na daga cikin gwamnonin da ke wakiltar Najeriya a taron. Ya ce wajibi ne a tsara ayyukan raya karkara domin cimma burin da aka sa gaba.

Matasa na da rawar takawa a sabuwar tafiyar da gwamnonin jihohin tafkin Chadi suka sa gaba, dalilin da ya sa aka gayyato shugabanin kungiyoyin matasan wadannan kasashen, inda Kwamred Dauda Mohammed Gombe ya fito daga Najeriya.

Wakiliyar tafkin Chadi, Ambasada Hadiza Mustapha, ta shaida wa wakilin Muryar Amurka, cewa tarayyar Afirka ta jaddada goyon bayan wannan tsari don zai kawo samun zaman lafiya a yankin tafkin Chadi.

Da yake jawabin bude taro Firai Ministan Nijar Birgi Raffini ya ja shawarci mahalarta taron da su natsu domin kawo shawarwarin da za su ba da damar daukar matakan da za su taimaka a kawo karshen kuncin rayuwar da miliyoyin jama’a suka shiga a yankin na Tafkin Chadi.

Ga cikakken rahoton wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma.

Your browser doesn’t support HTML5

Tattalin Arziki: An Bude Taron Gwamnonin Jihohin Yankin Tafkin Chadi