Sanar da kudin sayar fom na nuna sha’awar takara ke da wuya, wadansu daidaikun jama’a da kungiyoyi su ka fara fita suna nuna cewa sun saya ko kuma za su saiwa wadansu masu sha’awar tsayawa takara kudin fom, da ake ta kushewa da cewa ya yi tsada.
Daga cikin fitattun ‘yan siyasa a Najeriya da aka ce an biya wa kudin fom din akwai, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, da tsohon gwamnan jihar Lagos, kuma jagoran jam’iyar APC mai mulki Asiwaju Bola Tinubu. Sauran kuma sun hada da gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal, da tsohon gwamnan jihar Anambra Peter Obi da tsohon shugaban majalisar dattijai Bukola Saraki.
Wata kungiya mai kiran kanta “Asiwaju Project Beyond 2023” ta bayyana niyar biya wa tsohon gwamnan jihar Lagos Bola Tinubu kudin fom din neman tsayawa takara, karkashin tutar jam’iyar APC. A sanarwar da kungiyar ta fitar ta hannun jami’in sadarwar ta Adeboye Adebayo ta bayyana cewa, suna da kwarin guiwa ganin irin rawar da tsohon gwamnan ya taka a lokutun baya, zai kai Najeriya tudun mun tsira.
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya kuma dan takarar shugaban kasa na Jam’iyar PDP a zaben 2019 Atiku Abubakar ya sanar a shafinsa na twitter cewa, wata kungiya ta biya mashi Naira miliyan 40 kudin neman takara karkashin tutar jam’iyar PDP.
Shugaban Kungiyar da ake kira dandalin ‘yan kasuwar Arewa maso gabashin Najeriya Alhaji Dalhatu Funakaya ne ya mika fom din ga tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar.
Haka kuma wata kungiyar abokai karkashin jagorancin babban lauya Aree Olumiyiwa Akinboro ta ce, ta biya wa gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal, kudin fom domin neman tsayawa takara karkashin tutar jam’iyar PDP.
Wata Kungiyar kuma da ake kira Kungiyar Matasa Kwararru ta saya wa Peter Obi fom din neman tsayawa takara karkashin tutar jam’iyar PDP, yayinda wata kungiya da ta ce tana fafatukar kare mutuncin matasa ta ce ta saya wa tsohon Shugaban Majalisar dattawa Bukola Saraki fom din neman tsayawa takara kamar yadda shugaban kungiyar Abubakar Danmusa ya bayyana.
Sai kuma wata kungiya da ta ke kiran kanta Kungiyar goyon bayan Amaechi (ASG), ta bayyana neman Ministan sufurin ya tsaya takarar shugaban kasa a babban zaben 2023.
Banda masu neman tsayawa takarar shugabancin kasa kuma, kwamishinan watsa labarai na jihar Plato Yakubu Datti ya sanar da cewa, kwamishinonin jihar sun hada kudi Naira miliyan 60 sun biya wa gwamnan jihar Simon Lalong kudin fom din neman tsayawa takarar majalisar dattijai.
Jam’iyun siyasar Najeriya da dama sun bayyana niyar yin rangwami kan kudin fom din, da ya hada da dauke wa mata da matasa da kuma masu fama da wata lalura kudin fom din baki daya idan ta kama, da nufin karfafa masu guiwa, da basu damar tsayawa takara.
‘Yan Najeriya da dama suna gani da walaki a batun ikirarin sai wa ‘yan siyasar kudin fom na neman tsayawa takara. Daga cikin masu fada a ji da su ka kushewa wannan salon akwai tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, wanda ya shaidawa ‘yan Najeriya kada su zabi duk mai neman tsayawa takarar da ya ke ikirarin cewa an sai mashi fom, Bisa ga cewar shi, duk dan takarar da ya gayawa ‘yan Najeriya cewa an saya mashi fom karya ya ke yi, sabili da haka ya kamata a guji irin wadannan mutanen basu cancanci yin shugabanci ba idan ba za su gayawa ‘yan Najeriya gaskiya ba.
Banda salon saiwa masu sha'awar tsayawa takara fom, ‘Yan Najeriya suna kushewa tsadar kudin fom ga masu sha’awar tsayawa takarar zaben shekara ta 2023, da wadansu ke dorawa kan shugaba Muhammadu Buhari.
Masu wannan ra’ayin suna la’akari da karin da aka samu ninkin ba ninki na kudin fom din daga lokacin da Shugaba Buhari ya fara tsayawa takarar shugaban kasa, da a wancan lokaci shi da kanshi ya koka kan kudin fom din da ya ce ya yi tsada
Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, sai da ya sami fahimta da kuma hadin kai daga wajen Bankin shi a Kaduna kafin ya iya biyan kudin form din naira miliyan 27.5 na neman takara karkashin tutar jam’iyar APC a shekara ta 2014.
A ganawarshi da manema labarai a Abuja bayan sayen fom din a wancan lokacin, shugaba Buhari ya bayyana cewa, ya yi kokarin neman a rage kudin fom din amma bai sami goyon bayan ba. Bisa ga cewarshi, ya kira shugabannin bankin ya bayyana masu halin da ake ciki, yace “Naira Miliyan 27 kudi ne mai yawan gaske, abin godiya, ina da kyakkyawar dangantaka da manajan banki na a Kaduna, da sassafe yau na buga mashi waya na gaya mashi cewa nan ba da dadewa ba fom zasu iso, ko ajiya ta na cikin ja ko kore ko ma baki ne idan ka yarda ka lamunta, idan ba haka ba zan rasa damar neman tsayawa takara”
A wata hira da manema labarai bayan biyan kudin fom din, shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, zai biya rancen da ya karba daga banki domin sayen fom din neman tsayawa takarar ne daga gidauniyar neman gudummuwar ‘yan karo-karon masu taro da sisi da aka kafa.
A shekara 2018 jam’iyar APC ta kara kudin fom dinta zuwa Naira miliyan 45. A lokacin an bada rahoton cewa, wata kungiya ta saya wa shugaba Muhammadu Buhari fom din sake tsayawa takarar shugaban kasa domin neman wa’adin mulki na biyu, bayan shekaru hudu yana shugabancin Najeriya. A lokacin da ya sanar da niyarsa ta sake tsayawa takara, jam’iyar APC reshen Birtaniya ta bakin kakakinta Jacob Ogunseye ta bayyana cewa zata dauki nauyin saiwa shugaban kasar fom din neman sake tsayawa takara, sai dai babu tabbacin ko kungiyar ce fadar shugaban kasa ta ke ambato lokacin da ta bayyana ta bakin kakakin fadar shugaban kasa Garba Shehu cewa, wata kungiya ce ta biya kudin fom din.
A nata bangaren, babban jam’iyar hamayya PDP ta saida kudin fom din neman tsayawa takarar lokacin tana mulki a kan Naira miliyan 22 a shekara ta 2014, ta kuma sayar da shi kan Naira miliyan 12 a zaben 2019, yayinda ta ke saida fom kan Naira miliyan 40 kasa da rabin kudin sayen fom na jam’iyar APC. A dukan shekarun, kudin sayen fom din nuna sha’awar tsayawa takara na jam’iyar APC yana fin na jam’iyar PDP.
Ku Duba Wannan Ma Damokaradiya, Siyasa, Da Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa A Najeriya