Tasirin Rikicin Libya Kan Sauran Ƙasashen Afirka

Harin Da Aka Kaiwa Dakarun Faransa Da Mali a Garin Gao

Taron da ministocin tsaro na ƙasashen yankin Sahel suka gudanar a Abuja ya ƙara fitowa da batun illar da fitinar da ta kai ga kashe Shugaba Mu'ammar Gaddafi ta haddasa, inda 'yan ta'adda da makamai suka bazu a kasashen yankin.

Hatta tsanantar kashe-kashe a Binuwai ma a bayanin Shugaba Buhari ba zai rasa nasaba da irin waɗannan 'yan ta'addan ba.

Ministan tsaron Nijar, Kalla Muntari ya bayyana yadda abun takaicin ke shafar tsaron yankin, ya na mai cewa, saka jami'an Libya a irin wannan tattaunawa zai taimaka wajen rage ƙalubalen.

Ministan tsaron Najeriya, Mansur Dan Ali a nasa bangaren ya ce, ba tura jami'an tsaro ne kaɗai zai taimaka ba, akwai buƙatar inganta rayuwar al'umma ta hanyar shugabanci mai nagarta.

Bala Muhammad Maradun daga Zamfara, ya ƙara ƙarfi kan wannan matsaya da nuna lalle talauci na daga ginshiƙan samun miyagun iri.

Wani ƙalubalen shine hucewa kan matafiya da ba su ji ba ba su gani ba da miyagu ke yi sakamakon wata fitina a ƙauyuka. Irin wannan dai kan sanya ayar tambaya kan tasirin jami'an tsaron da ke tsayawa a kan manyan hanyoyi baya ga haddasa jinkiri ga matafiya da neman na goro.