Tamkar kalandar giringori wadda ake kira Gregorian calender a turance, wadda ta kunshi wata 12 daga Janairu zuwa Disamba, ita ma kalanda ko shekarar Musulunci ta kunshi wata 12 farawa da Muharram zuwa Zulhijjah.
Sai dai babanci shi ne watannin kalandar musulunci ana iya ganin su a sararin samaniya kuma soma kidayar wata ya ta'allaka ga ganin jinjirin wata inda watan zai iya kwana 29 ko 30, sabanin ta giringori wadda ke da kwanan wata 30 ko 31 da 28 ko 29 a watan Fabrairu, abin da ya sa ta fi shekarar Musulunci tsawon kwanaki.
Akasarin kasashe na duniya sun karkata ga amfani da kalandar giringori wajen tafiyar da lamurran yau da kullum, sai dai kuma akwai wasu kasashe na Musulmi da ke amfani da kalandar Musulunci.
Duk da karamin kulawa da wasu ke baiwa kalandar ta musulunci, malamai sun ce tana da tasiri sosai, Dr. Mustapha Sidi Attahiru malamin Musulunci ne a Najeriya, ya ce amfani da kalandar musulunci za ta hada kan musulmai a ko'ina, kuma al’amuran musulunci zai zama daya a ko’ina a fadin duniya.
Yanzu duk da lamurran Musulunci sai an yi amfani da sunan watan na giringori, kamar ranakun da ake kebewa na hutu a shekara ko da hutun ya shafi wani aiki na Musulunci, to ya za’a iya samun sauyin wannan lamarin?
Muhammad Lawal Maidoki yana cikin masu fafutuka akan girmawa tare da yin aiki da kalandar musulunci a Najeriya, ya ce za a Iya kaiwa lokacin da gwamnatoci a Najeriya za su yi amfani da wannan kalanda wajen biyan albashi a wurin aiki.
A wasu yankuna na Musulmi duk da yake ana amfani da kalandar giringori, ana gwama kalandar Musulunci kamar a makarantu ko kafafen yada labarai duk domin kara samar da tasirin shekarar ga jama'a.
Saurari rahoto cikin sauti daga Muhammadu Nasir:
Your browser doesn’t support HTML5