Wannan ya nuna kari daga alkaluman baya na kashi 29.90%.
Idan an kwatanta da bara, daidai Febrairu an samu karin kashi 9.79%.
A hirar shi da Muryar Amurka, wani talaka Muhammad Salisu ya nuna damuwa kan kuncin da talakawa ke ciki.
Bayanan kungiyar ta NBS sun nuna sashin kudu maso yammacin Najeriya ya fi tsadar abinci inda arewa maso yamma ya fi samun rangwame.
Mai taimakawa Shugaba Tinubu kan labaru Abdul'aziz Abdul'aziz ya ce don magance kunci ne ya sa Shugaba Tinubu ganawa da shugabannin kasashe masu arziki don zuba jari a Najeriya kamar yadda ya faru kwanan nan a Daular Larabawa.
Tun cire tallafin man fetur da Shugaba Tinubu ya yi a ranar 29 ga Mayun bara a ke samun karin tsadar rayuwa a Najeriya.
Sai dai a bayaninsa, masanin tattalin arziki kuma shugaban 'yan arewa mazauna kudu Ambasada Musa Sa'idu ya ce kalubalen ya wuce na cire tallafin.
A Najeriya dai yanzu ga zafin rana ga na aljihu sai jiran tsammanin alkawarin sauki.
Saurari rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5