Tashen Watan Ramadana a Kasar Hausa

Yara sun yi shirin tashe

Da shiga goma ta tsakiya na watan Ramadana, lokaci ne da matasa da yara suke yin tashe.

Da zarar an shiga 10 ta tsakiya a watan Ramadana, lokaci ne da ake yin tashe, ma’ana, a mafi yawan lokuta matasa ko yara kan canza shigarsu ta hanyar shafa wasu abubuwa a fuskarsu da jikinsu suna shiga lungu-lungu da sakosako suna wasa na barkwanci.

Akan bai wa masu tashen taro da sisi a kusan duk inda suka je.

Ana dai fara tashe ne bayan an sha ruwa ana kuma zuwa majalisu da gidaje, don nuna wasu dabi’u marasa kyau ko masu kyau domin fadakarwa.

Tashe na daga cikin al’adun bahaushe kuma mafi yawa wannan al’ada na neman gushewa, ko da yake yaran da muka zanta da su sun bayyana cewa a talabijin suka gani suka kuma yi sha’awar wannan tashe.

Malamai sukan ce addini bai hana duk wani abu da ya zo ba, matukar bai sabawa addinin musulunci ba, don haka ya ce wannan wata hanya ce da take kawo nishadi da walwala.

Saurari cikakken rahoton Baraka Bashir daga Kano domin karin bayani:

Your browser doesn’t support HTML5

Tashen Watan Ramadana a Kasar Hausa