Tashar CNN Ta Yi Nasara a Kotu Kan Fadar White House

Tashar CNN

Tashar labarai ta CNN ta yi nasarar karar da ta shigar kotu game da soke izinin wakilinta na shiga da dauko rahoto a fadar shugaban kasar Amurka ta White House.

Kotu ta umurci Fadar Shugaban Amurka ta White House da ta maida wa wakilin gidan talabijin na CNN, Jim Acosta takardar izinin shiga da kuma dauko labarai daga Fadar ta White House, wadda aka soke bayan wata sa'insa tsakanin dan jaridar da Shugaba Donald Trump a yayin wani taron manema labarai a fadar.

"Zan amince da bukatar soke matakan da Fadar Shugaban kasa ta dauka na wuccin gadi," kamar yadda gidan talabijin na CNN din ya bukaci a yi, a cewar Alkalin Kotun Gunduma Timothy Kelly a jiya Juma’a. Ya kara da cewa, "Na umurci gwamnati ta mai da wa dan jaridar takardun izinin shiga Fadar."

Alkali Kelly, wanda ya yi nuni da abin da ya kira, "wasu tabbatattun batutuwa masu sarkakkiya," ya ce shi ya na yanke shari'a ne kawai kan gyara ta 5 na kudin tsarin mulki kan batun ka'ida a wannan batun, amma ba kan daukacin Gayar da farko ba.

Da yake magana bayan yanke hukuncin dan jarida Jim Acosta, ya ce “Ina mai godiya ga wannan alkalin da ya yanke hukuncin, lokacin komawa bakin aiki yayi.