Shugaban Amurka Donald Trump ya hadu da Firai ministar Birtaniya Theresa May da Firai ministan Canada Justine Trudeau da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da sauran shugabannin duniya a birnin Portmouth da ke kudancin Birtaniya, domin tunawa da dakarun hadakar kasashen nahiyar turai da suka yi taron dangi suka kuma samu nasara akan sojojin Nazi.
Taron ya kunshi kade-kade da karanto tarihin abin da ya faru a lokacin, ciki har da inda Shugaba Trump ya karanta addu’ar da tsohon shugaban Amurka Franklin Roosevelt ya taba karantawa ga masu sauraren rediyo, bayan da aka fara mamayar sojojin na Nazi a shekarar 1944.
Ita ma Sarauniyar Ingila Elizabeth ta 2 ta shiga cikin taron tare da tsoffin dakaru da suka taka rawa a wannan rana, wacce ake wa lakabi da D-Day.