Taron Tattaunawa Game Da Zaben Jamhuriyar Nijar

Taron Tattaunawa Kan Zaben Jamhuriyar Nijar

Muryar Amurka ta shirya wani taron tattaunawa a birnin Yamai, karkashin jagorancin Ibrahim Ka-Almasi Garda, game da yadda za a gudanar da zaben ranar 21 ga wannan wata na Fabarairu.

Wannan taron da ya kwashe kusan sa'o'i biyu, ya gayyato masu ruwa da tsaki wanda suka hada da shugabanin kungiyoyin Fararen Hulla da wakilan bangarori daban-daban na jam'iyyun siyasa da matasa har ma da kungiyoyin Addinai da dai saurensu.

Inda baki bangarorin suka tattauna kan hanyar da kowa zai iya bayar da gudunmawar sa domin a gudanar da wannan zabe a cikin gaskiya da lumana. An dai kammala taron a cikin raha tare kuma da fahintar juna tsakanin bangarorin da suka halarta.

Daya daga cikin wadanda suka halarci wannan tattaunawar Alhaji Salisu Ahmadu, ya bayyana irin tasirin da wannan tattaunawar zatayi game da shirya zabe da gudanar da shi cikin kwanciyar hankali. Ya kuma baiwa Muryar Amurka shawarar ci gaba da gudanar da irin wannan taron kan fannoni daban daban da suka shafi kasar jamhuriyar Nijar.

Saurari rahotan da Yusuf Abdoulaye daga Yamai.

Your browser doesn’t support HTML5

Taron Tattaunawa Game Da Zaben Jamhuriyar Nijar - 3'07"