Irin hayaniyar da ta barke kenan tsakanin wakilan jam’iyu masu mulki da na jam’iyun kawancen adawa a yayin taron majalisar CNDP mai alhakin tantaunarigingimun siyasar kasar.
A wannan haduwa ta yammacin Talata batutuwa hudune ke kan teburin shawara sai dai maganar sake duba tsarin jadawalin zabe ita ta mamaye wannan tantaunawa inda aka shafe awoyi 3 ana zazzafar mahawara tsakanin bangarorin siyasar biyu.
Su dai ‘yan adawa dake bukatar a yiwa ajandar zaben gyaran huska suna zargin masu rinjaye da laifin kamakarya akan wannan batu kamar yadda Sabo Saidu na jam’iyar MDC yarda ta bangaren adawa ke cewa.
A nasu bangare jam’iyun kawancen dake mulki sun musanta wannan zargi. A cewar Yahaya Abdu na jam’iyar PNA al’uma haddasa cijewar al’amuran shirye shiryen zabe shine burin ‘yan adawa .
To sai dai shugaban jam’iyar moddel ma’aikata ta gungun jam’iyun dake mulkin Nijer Alhaji Tahiru Gimba na mai ganin idan kusu da sata to daudawa ma da wari.
Yanzu dai ana iya cewa kallo ya koma wajen hukumar zabe ta kasa wace dokokin zaben Nijer suka baiwa wuka da nama akan dukkan wasu batutuwan da suka jibanci shirya zabubuka a kasar.
Ga rahoton Sule Barma.
Your browser doesn’t support HTML5