Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Talakawan Jamhuriyar Nijar Basa More Arzikin Ma'adanan Kasarsu


Shugaba Mahamadou Issoufou na Jamhuriyar Nijar
Shugaba Mahamadou Issoufou na Jamhuriyar Nijar

Jamhuriyar Nijar kasas c da Allah ya albarkaceta da ma'adanan kasa iri-iri.

Kasar tana da karfen uranium da zinariya da gawayi da man fetur da ma wasu da dama.

To saidai bayanai na nunawa a fili talakawan kasar basa more arzikin da Allah ya basu sakamakon sakacin mahukuntan kasar na jiya da na yau. Wannan ko ba zai rasa nasaba da yadda su ke rufe idanunsu da rashin adalcin kamfanonin dake hakansu kaman irinsu ariva da kasar Faransa da cmpc na kasar China.

Wani rahoton binciken kare hakin bil Adama ya bayyana hakan. Rahoton ne ya sa hukumar kare hakin bil Adama ta cndh ta tashi haikan domin tunkarar matsalar.

Mai shari'a Ahmadu Ali Shina Kurgeni babban sakataren hukumar kare hakin dan Adam ta kasar Nijar ya bayyana irin illar da hakan ma'adanan ke jawowa talakawa. Misali ruwan dake gangarowa daga inda ake hakan zinari mutane na shan shi kuma yana zaman masu lahani.

Masu hakan ma'adanai basu damu da gurbacewa muhalli ba saboda hukumomin kasa basu mayar da hankalinsu kan tsaftace muhalli ba.

Kungiyoyin fararen hula sun dade suna fafutika da yakar dabi'ar yin fatali da dokokin hakar ma'adanan kasa.

Dalili ke nan da hukumar kare hakin dan Adama ta Nijar da takwararta ta kasar Denmark suka gayyato shugabannin kungiyoyi masu zaman kansu taron karawa juna ilimi.

Ga rahoton Sule Mummuni Barma.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:38 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG