Malaman Jami’oin Musulunci da Malaman addinin Islama, sun Tauttauna akan tanaje-tanaje da hukumce-hukumce a kan dokoki kan yadda ake bada agaji kamar yadda shari'ar musulunci ta tsara a matsayin ingantancciyar hanyar samun sassauci mussammman ga waddanda lamarin ya shafa.
Malaman dake halartar taron sun tattauna a kan yadda za a kula da waddanda suke da matsaloli sosai, sun kuma tattauna mussamman a kan yadda za a kula da yara da mata da marayu.
Ministan ilimi mai zurfi na Jamhuriar Nijer, Yahuza Salisu ya kalli wannan taro a matsayin taro mai matukar tasiri, ya kuma bayyana cewa yana fatan mahalarta taron za su kawo shawarwari ta yadda za’a magance matsaloli da kuma rigakafin kaucewa fitina.
Da yake ci gaba da bayani, Ministna ya kara cewa ce za su dubi abinda malaman Islama suka kawo, za kuma su tantance su, hadi da nasu binciken, daga bisani su dauki na dauka sa'annan su jingine na jinginewa.
Wannan Taron shine karo na biyu da kungiyar agaji ta CICR da malaman jami’oin Musulunci ke hallara a daki daya domin kara wa juna sani da nufin neman hanyoyin takaita wahalhalun da waddanda yaki ya shafa.
Wakilin muryar Amurka a Yamai Sule Mumuni Barma ya aiko mana Karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5