Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Rajin Kare Hakkin Bil Adama Sun Kira Uganda Ta Kama Shugaban Sudan Bashir


Shugaban Sudan Omar Bashir yayinda ya sauka Entebe babban birnin Uganda inda yake ziyarar kwana biyu
Shugaban Sudan Omar Bashir yayinda ya sauka Entebe babban birnin Uganda inda yake ziyarar kwana biyu

Tun shekarar 2009 kotun manyan laifuka ta kasa da kasa ko ICC ta samu Shugaban Sudan Omar Bashir aikata laifuka biyar da sun jibancicin zarafin dan Adam kuma tun daga lokacin take nemana a kamashi

Masu fafutukar kare hakkin bil adama, suna kira ga hukumomin Uganda da su kama shugaban Sudan Omar al-Bashir, wanda yake ziyarar aiki ta kwanaki uku a kasar, suna masu neman da a mika shi ga kotun hukunta manyan laifuka ta ICC domin ya fuskanci tuhuma.

A shekarar 2009 kotun ta ICC ta samu shugaba Bashir da aikata laifuka biyar da suka jibinci cin zarafin bil adama, sannan aka same shi da wasu laifuka biyu na aikata laifukan yaki a rikicin da ya faru a yammcin Darfur.

Har ila yau a shekarar 2010, an caje shi da laifin aikata kisan kare dangi a rikicin na Darfur.

Shugaban kungiyar kare hakkin bil adama na Human Rights Network, Mohammed Ndifuna ne ya karanta wata sanarwa a madadin wasu dumbin kungiyoyin kare hakkin bil’adama na Uganda.

Sai dai, mai magana da yawun gwamnatin Uganda, Ofwono Pondo, ya ce ba za su iya kama shugaban wata kasa mai ci ba.

Opondo har ila yau, ya fadawa shirin South Sudan in Focus cewa, sun yi amanna shugaba Al Bashir na taka rawar gani wajen wanzuwar zaman lafiya a yankin.

Shi dai Al Bashir ya ziyarci kasashen Afirka da dama, tun bayan da kotun ta ICC ta same shi da aikata laifukan yaki, kasashen da suka hada da Chadi da Afirka ta Kudu da kuma Sudan ta Kudu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG