Wannan taro dai ya hada da wakilan kasashen Chadi da Tunisia da Masar da Mauritania da Algeria da Nijar da Sudan, haka kuma taron ya samu halartar wakilan tarayyar Afirka da na Tarayyar Turai, harma da wakilin MDD a kasar Libya, don neman hanyar samar da mafita ga kasar ta Libya.
A cewar ministan harkokin wajen Nijar Ibrahim Yakubu, abin da suka gani shine a saka gwamnatin da kowa ya amince da ita, kasancewar gwamnatin dake ci yanzu ta kasa zama da gindinta sanadiyyar babu wanda ya amince da ita. Abu na gama kuma shine bayan an kafa gwamnati mai cikakkiyar iko kuma kowa ya amince da ita, sannan a samar da rundunar soja.
Taron na ministocin harkokin wajen kasashen da ke makwabtaka da kasar Libya wanda yake gudana a washegarin wanda kwararru suka gudanar, ya bullo da wasu sabbin shawarwari, bayan la’akari da cewar sun fi kowacce kasa ‘dan ‘dana kudar irin abubuwan da ke faruwa a kasar Libya.
Wakilin MDD ya bayyana cewa amfani da karfin soja ba zai taimaka a warware rikicin kasar ba, saboda haka dole ne abi hanyar tuntuba tsakanin bangarorin da basa ga maciji da juna, domin cimma dai daiton da zai bayar da damar kafa wata gwamnatin hadin kan ‘yan kasa.
Ga rahotan Sule Mumuni Barma daga Nijar.
Your browser doesn’t support HTML5