Kudirin ya tanadi kafa gwamnatin wucin gadi a kasar saidai babbar jam’iyyar adawa ta kasar ba ta amince da shirin ba.
Bayan wata daya da rabi da aka kwashe ana wannan ganawar, wakilai 300 ne suka fito da Kudirin da niyyar kawo karshen rikicin siyasar dake faruwa a Janhuriyar Dimokaradiyya Congo. Hukumar zaben kasar kuma ta ce ko kusa ma bata shirya ba domin zaben da aka shirya za'a yi cikin watan Nuwamba mai zuwa.
Babar jam’iyyar adawa da ta kauracewa ganawar, tana zargin shugaba Joseph Kabila da ya kwashe shekaru 15 akan karagar mulkin kasar da ke tsakiyar nahiyar Afrika, da neman tsawaita wa’adin mulkin sa ba bisa ka’ida ba.
Wata daya da ya wuce ne aka yi wasu munanan zanga zanga a kasar inda har mutane 56 suka mutu aka kuma kona wasu helkwatocin jam’iyyun siyasa.
Sabon Kudirin ya yarda shugaba Kabila ya cigaba da zama kan kujerar mulkin kasar har sai anyi zabe, amma za'a nada firayin minista daga banagaren 'yan adawa.