Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Nijar Ta Gabatar Da Kasafin Kudin Shekarar 2017


APTOPIX Niger Elections
APTOPIX Niger Elections

Kasafin kudin na shekarar 2017, yana akan Miliyan dubu dari daya da dari takwas da tara na Sefa sabanin na shekarar 2016 da ake ciki, wanda yake sama da miliyan dubu daya, da dari takwas.

Wannan ya nuna cewa an samu Karin miliyan dubu biyu na sefa idan aka kwatanta shi dana shekarar nan.

Karamin ministan dake kula da kasafin kudi Amadu Judud ya bayyana wa majilisar dokokin jamhuriyar Niger cewa kasafin kudin na shekarar badi zaifi mayar da hankali ne akan ayyukan sake farfadowa da kasar ta Niger da ake kira RENASENSIDE.

To sai dai tuni ‘yan majilisar dokoki bangaren adawa suka yi watsi da kasafin kudin.

Sumani Sanda shine shugaban jamiyyar Lumana dake bangaren adawa.

‘’Birjet ya wuce kunga miliyan dubu da dari takwas, amma abinda suka tara shine miliyan dubu dari biyar da hamsin da daya, Kenan kunga ba a tara kudi ba, amma tunda ana son a nuna wa ‘yan kasa kullun aiki akeyi’’….

Ga Yusuf Abdullahi da Karin bayani 2’16

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:16 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG