Taron kasashe rainon Ingila a Australia

  • Ibrahim Garba

Firayim Ministan Burtaniya David Cameron

Kasashe da dama da ke da alaka da tsohuwar daular Burtaniya sun

Kasashe da dama da ke da alaka da tsohuwar daular Burtaniya sun kasa cimma matsaya game da batutuwa da dama na hakkin dan adam.

An kammala taron na kwanaki 3 na kasashe rainon Ingila a jiya Lahadi a birnin Perth na Australia. Shugabannin sun ce sun dan sami cigaba wajen aiwatar da sauye-sauye, to amman matakan bas u kai yadda wasu kasashen su ka sa rai ba.

Alal misali, kingiyar kasashe 54 din ta dage batun yanke shawara kan ko za ta kirkiro wani sabon mukami na kwamishinan Dimokaradiyya, da Aiki da Doka da kuma Hakkin Dan Adam. Jami’an hukumar za su bi diddigin take hakkin dan adam a kasashen da ke cikin kungiyar su kuma bayar da shawara kan irin hukuncin da su ke ganin ya cancanci duk wata kasar da ta cigaba da kuntata wa mutanenta.

Kasashen da su ka ki amincewa da kirkiro mukamin kwamishinan sun hada da Indiya da Afirka ta Kudu da Sri Lanka.

An bai wa Sri Lanka damar daukar nauyin taro na gaba da za a yi a 2013. To amman Firayim Ministan Canada Steven Harper y ace zai kaurace wa taron sai inko gwamnatin Sri Lanka ta binciki laifukan yakin da sojojinta suka aikata a cikin wata na karshen yakin basasarta.