Manjo Hamza Al-Mustapha yayi magana wajen taron sanya hannu a yarjejeniyar kafa jami’ar tsaro da hadin gwiwar jami’ar Abuja, saboda koyon dabarun kaudabara daga ‘yan ta’adda musammam ma ‘yan Boko Haram.
Al-Mustapha wanda yake tsohon jami’in tsaro ne da yayi aiki da Janal Sani Abacha, yace wannan nau’in jami’ar tsaro zata zama ta farko a Najeriya da ma nahiyar Afirka.
Manjo Al-Mustapha ya tallafawa jami’ar Abuja da wasu motocin safa don jigilar ‘dalibai, da hakan zai share fagen fara aikin wannan jami’ar, da samo kwararru daga gamayyar cibiyoyin asiri na tsaron Najeriya.
In za a tuna dai tsohon shugaba Jonathan yace da makaman da yayi oda ne ake amfani wajen yaki da Boko Haram, yana mai cewa a shirye yake ya tallafawa gwamnatin Buhari a duk inda ya dace ko kuwa ake ganin zai iya bada gudunmawa.
Your browser doesn’t support HTML5