Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tawagar Shugaba Buhari Ta Je Jaje Kauyen Dalori


Wata tawaga da shugaban kasa ya kafa karkashin jagorancin sakataren gwamnatin jihar tarayya Injiniya Baba Chir David Lawal, don jajantawa al’ummar kauyen Dalori da wasu mahara suka kaiwa hari a ranar Asabar din da ta gabata wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane da kuma raunata wasu dayawa.

Tawagar dai ta ziyarci wannna kauye na Dalori inda suka ganewa idanunsu irin yadda wannan mahara sukayi barna, da kuma jajantawa mutanen wannan kauye, harma da yin addu’a ga wadanda suka raunata.

Bayan ziyartar wannan gari ne dai sakataren gwamnatin tarayya Injiniya Baba Chir David, ya yiwa al’ummar wannan gari jawabi, inda ya gaya musu cewa shugaban kasa ne ya aiko su domin yiwa mutanen yaje.

Wakilin Muryar Amurka ya lura da wasu ‘dai ‘dai kun jama’a a kauyen wanda ke zaune bakin bishiya, yayinda kusan dukkannin gidajen dake wannan kauye sun kasance tamkar kango. Wasu mazauna garin sun bayyana halin da suke ciki tun bayan harin, inda sukace matsalar abinci da ruwan sha ke damunsu gashi an kone musu gidajensu.

Tawagar dai sun ziyarci asibitoci da ke cikin garin Maiduguri, wanda suka hada da asibitin koyarwa da na kwararru don jajantawa mutanen da if’tila’I ya shafa. Sai dai babu wani tallafi ko kuma alkawari da wannan tawaga suka yi wa mutanen.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:38 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG