Amurka Da Jihar Sakkwato Sun Shirya Taron Ilimin Mata

Wasu Mata 'Yan Najeriya

Ofishin Jakadancin Amurka tare da hadin gwiwar hukumar adana kayan tarihi na Waziri Junaidu a jihar Sokoto, sun gudanar da wani taro don inganta harkokin ilimi da gudumawar da mata ke bayarwa.

Taron ya hada manyan baki masu ruwa da tsaki a sha'anin ilimi yayin da Jakadan kasar Amurka ya samu wakilcin jami'in da ke kula da fannin al'adu da rubuce-rubuce da ilimi, Lawrence Salcher.

Taron ya mayar da hankali kan matan Arewacin Najeriya a fannin Ilimi da sha'anin rubuce-rubuce, da kuma zakulo kalubalen da ya dabaibaye sha'anin ilimin 'ya'ya mata, wanda kawo yanzu yana ci gaba da zama barazana ga yankin Arewacin Najeriya.

Wani malami a sashin nazarin tarihi a Jami'ar Usman Dan Fodiyo a jihar Sokoto, ya gabatar da makala kan kalubalen da ilimin 'ya'ya mata ke fuskanta. Yace yankin Arewacin Najeriya yanki ne da ilimin addinin Musulunci ya riga na zamani zuwa.

Wanda kuma ya kasance ilimin addinin Musulunci yana da tsarin rarrabewa tsakanin mata da maza, shi kuma ilimin zamani na da tsari na dabam. Taron ya duba gagarumar gudunmawar da mata ke bayar wa kan harkar ci gaban rubuce-rubuce da na ilimin zamani a Najeriya baki daya.

Ga rahotonmu nan cikin murya daga kasa don saurare.

Your browser doesn’t support HTML5

Taron Ilimi Mata Da Rubuce Rubuce A Jihar Sokoto - 2'52"