Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Najeriya Ya Kai Ziyarar Jaje Jihar Bauchi


Shugaban Najeriya Muhammad Buhari
Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya kai ziyarar gani da ido da yin jaje zuwa jihar Bauchi biyo bayan gobarar da ta rutsa da kasuwar Azare tare da bala’in ambaliyar ruwa da wata muguwar guguwa da suka addabi Bauchi suka kuma yi sanadiyar mutuwar mutane takwas

Shugaban da ya sauka a filin jirgin sama dake garin Bauchi ya zarce zuwa Azare domin ganin irin barnar da gobara ta yiwa kasuwar garin.

Haka kuma shugaban ya ziyarci fadar sarkin Bauchi, Alhaji Rilwanu Suleimanu Adamu inda ya mika gaisuwarsa.

Yace ya ga irin barnar da gobara ta yi a kasuwar Azare da fatan Alla zai maida masu abun da ya fi asarar da suka yi. Ya karfafa musu gwiwar yin addu’a saboda bala’in da ya faru ya fi karfin mutum

Shugaba Buhari ya yiwa wadanda abun ya shafa jaje da ta’aziya.

Shi ko gwamnan Bauchi Barrister Muhammad Abdullahi Abubakar ya bayyana ziyarar ta shugaban kasa a matsayin ta soyayya ce. Ya ce tun kafin shugaban ya kawo ziyarsa ya ce a mikawa mutanen jihar jajensa. Bayan haka shugaban ya aika da wata tawaga a karkashin jagorancin ministan ilimi da shugaban hukumar bada agajin gaggawa zuwa jihar.

Gobarar ta lakume akalla shaguna dari biyar musamman, shagunan sayar da kayayyakin abinci da tufafi. Yawancin ‘yan kasuwan a Kano suke karbo kaya kuma sai sun sayar su mayar da kudin.

A saurari rahoton Abdulwahab Muhammad da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:00 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG