Daya daga cikin shugabannin, Malam Nuhu Arzika, ya ce kwalliya ta biya kudin sabulu domin sun nuna kukensu ga gwamnati.
“Allah da ikonsa ya ba da dama wannan taro an samu an yi shi lafiya an kare shi lafiya, sai mu yiwa Allah godiya taro dai ya yi kyau yadda muke so.”
A jiya Asabar aka gudanar da taron gangamin wanda aka shirya sa domin jan hankulan hukumomin Nijar kan batutuwan da ke ciwa mutane tuwo a kwarya.
“Na farko akwai matsaloli da dama da suka hada da matsalar rashin wutar lantarki da rashin ruwa da kuma rashin lafiya na ciwon sankarau wanda gwamnati ta nuna kamar ta kasa.” Inji Malam Arzika.
Ya kuma kara da cewa akwai batun karin mataimaka da aka kara a kasar bayan da hukumar kidayar kasar ta ce an samu dadin jama’a, wanda Arzika ya ce bai dace a yi wannan karin ba.
“Sannan akwai matsalar karin mataimaka inda aka ce an kara yawansu su kusan 60 a cikin wannan mawuyacin hali da mu ke ciki, muna mamaki a ce yaya za a yi ana jagoranci na gari a ce irin wannan abu na faruwa.
Domin jin karashen rahoto ga hirar Bello Habeeb Galadanchi da Malam Nuhu Arzika:
Your browser doesn’t support HTML5