Sabon shugaban Najeriya na shirin kai ziyara kasar Nijar makwafciyar kasarsa. Ziyarar zata zama ta farko da Shugaba Muhammad Buhari zai yi tunda aka rantsar dashi makon jiya.
'Yan Nijar sun bayyana ra'ayoyinsu akan shugaban da kuma shirin kai ziyara kasarsu. Wani yace Allah ne ya ba Muhammad Buhari mulkin Najeriya da fatan Allah ya tayashi riko. Sai dai ya roki Shugaba Buhari ya yi maganin 'yan Boko Haram da yace sun sha masu kai. Yayi addu'ar Allah ya kakkabe duk wasu azzalumi dake tare dashi.
Wani kuma fatan Allah ya kai Shugaba Buhari lafiya kasarsu ya yi. Yace ziyarar ta nuna Najeriya da Nijar kamar Danjuma da Danjummai ne suke. Yayi fatan kasashen da suke makwaftaka da juna zasu hada kawunansu da addu'ar Allah ya yi maganin Boko Haram.
Akan kasuwanci tsakanin kasashen biyu yace su kara dankon kasuwanci da yake tsakanin kasashen tun lokacin kakanni da kakanni.Kasashen su shiga kasuwanci irin na zamani ba irin na da ba. Gwamnatoci su yi hulda da juna domin a kawar da wasu matsaloli bisa hanyoyi. A samu a tsayar da doka guda da zasu amince da ita. Su tabbatar da kasuwanci tsakanin kasashen ba tare da wata matsala ba saboda bunkasa arzikinsu.
Ga karin bayani.