Kasashen Amurka da Japan da kuma Koriya ta Kudu ne suke kira wannan zaman gaggawar bayan Pyongyang din ta kaddamar da gwajin makami mai lizzami a jiya Lahadi mai cin dogon zango zuwa sama wanda ka iya harba rokar da zai ci nisan kilomita 4,500 ta sama.
Da safiyar yau Litinin, Korea ta Arewa tace ta yi nasara wurin kera sabon makami mai cin dogon zango a wani gwaji da shugaban kasar Kim Jong Un ya sa ido da nufin tabbatar da girma da nauyin makaman na nukiliya.
Kamfanin dillancin labaran kasar na KCNA yace an harba makamin ne ta sama yanda ba zai shafi tsaron kasashe makwabta ba kuma ya yi tafiyar kilomita 787 da nisansa ya kai tazarar kilomita 2,111 ta sama.
Kamfanin dillancin labarai na KCNA ya rawaito shugaba Kim yana zargin Amurka da tsoratar da kasashe da basu da makaman nukiliya, kuma ya yi kashedi ga Amurkan da ta daina bahaguwar fahimta a kan batun, da cewa, gaskiya lamarin shine, bangaren da take gwaje gwajen makaman yana cikin Koriya ta Arewa ne.
Fadar White tace gwajin makaman na baya bayan nan, yakamata ya zama kira ga kasashen duniya don aiwatar da tsauraran takunkumai a kan Korea ta Arewa.