Emmanuel Macron, shugaban Faransa mafi kuruciya tun tsohon shugaban kasar Napoleon Bonaparte, wanda ya ja ragamar mulkin Faransa fiye da shekaru maitan da suka shige, ya gabatar da kansa a matsayin shugaban dukkan Faransawa a yau Lahadi bayan an rantsar dashi a fadar Elisay. Yabi sahun tsaffin shugabanin kasar Janaral Charles De Gaulle da Jacques Chirac wajen yin wannan furuci.
Shugaba Macron tsohon ma’aikacin banki, wanda dududu shekaru biyu kawai yayi a matsayin Minista a gwamnatin wanda ya gada Francois Hullande ya fadawa Faransawa cewa burinsa shine ya hada kan yan kasar
Mutane miliyan ashirin da daya suka zabe shi a zaben fidda gwani da aka yi, to amma mutane miliyan goma sha biyu suka zabi abokiyar takarsa Marine Le Pen. Miliyoyi kuma basu kada kuri’a ba sa’anan miliyan hudu ne suka yaga takarun zaben su a zaman wata alamar rashin goyon bayan dukkan yan takaran.
Babar kalubalan dake gaban sabon shugaban shine samun goyon bayan yan Majalisar dokokin kasar da rinjaye. Ana kuma ganin samun hakan zai dogara ne akan wanda zai nada ya zama Prime Ministan sa a gobe Litinin idan Allah ya kaimu.
Facebook Forum