Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Pakistan Kunar Bakin Wake Ya Rutsa da Mutane 25 tare da Jikata Wasu 40


Harin kunar bakin wake
Harin kunar bakin wake

Wani dan kunar bakin wake ya tarwatsa wani ayari na ‘yan wata jam’iyyar Islamiyya a kudu-maso-yamamcin kasar Pakistan inda ya hallaka akalla mutane 25, wasu fiye da 40 suka sami raunukka.

Galibin duk wadanda abin ya shapa ‘yan wata jam’iyya ce mai suna Jamiat Ulema-e-Islam, wacce aka kafa ta a bisa akidar addiniNn Islama.

‘Yansanda sunce wannan farmakin da aka kai yau Jumu’a ya faru ne a garin Mastung, dake da tazarar kilomita 50 da Quetta, babban birnin lardin.

Ance an kai hari ne da nufin gamawa da wani kusar jam’iyyar ne mai suna Ghaforr Haideri, wanda shine ma mataimakin shugaban Majalisar Dattawan Pakistan.

Shi kansa Senator Haideri din an ji mishi ciwo a wannan harin, yayinda direbansa da wani mukarrabinsa dake rakiyarsa suka rasa rayukansu.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG