Limamin da ya jagoranci Sallar Eid fitr, a gundumar Bronx, dake birnin New York, ya bukaci iyaye da a tashi tsaye domin ganin cewar an tarbiyantar da yara kamar yadda yakamata .
Limamin yace” ‘Yan uwa maza da mata a madadin Malamai, ina mika wannan sako akan ‘ya’yan mu domin sune mayan mu a gobe, idan suka lalace toh me zai faru garemu saboda haka ya zama wajibi garemu mu tabbatar da ganin cerwa ‘ya’yanmu sun samu kyakkawar tarbiya.”
Horas da yara shine babban kalubale da yawancin Musulmi daga nahiyar Afirka, dake fuskanta a nan kasar Amurka, akwai yaran Musulmi masu tarin yawa wanda ilimi da aladu na kasanshen yamacin duniya yasa suka bujirewa addini da aladun iyayensu.
Wannan sun dalilan da yasa sakon Limamin akan tarbiyar yara ya samu karbuwa ga iyaye, kamar yadda wani magidanci Muhammad Aminu Muhammad, ke cewa “ Limamin mu yayi bayani kwarai babu abun da yafi burgeni kamar batin tarbiyar yara, tarabiyar yara a kasar Amurka yana da wahala shi yasa idan baka maida hankalin ka kan yaran nan kasar ba wallahi in kayi was kayi hasaran banza.”
Ita kuma Magajiyar Hausawa, a birnin New York, Hajiya Amina Bunkasa, cewa tayi”yakamata a kulla ya samanar cewar ko da wani lokaci ido na kan yara ana lura da abun da suke ciki, idan kana gudun zuciyar yaro wata rana kai zai dama.”