Ana sa ran manyan kungiyoyi hudu ne za su yi aiki tare da wasu kungiyoyin fafutuka, da jami’oi, da masu harkar ‘kasuwanci, da kuma ‘yan jarida domin inganta tsaron iyakokin kasar.
Hakan na zuwa ne bayan da masharhanta su ka yi gargadin cewa Ghana za ta iya fuskantar harin ta'addanci.
Kungiyon sun hada da Ghana Integrity Initiative, da BOK Africa Concern, da jami’ar ilimi ta Winneba, da kuma jami’ar Ghana da ke Accra.
Tallafin karfafa tsaron iyakokin Ghana da ke karkashin asusun lamunin gaggawa na tarayyar Turai wato European Union Emergency Trust Fund ko EUTF a takaice, ya kuma maida hankali akan kwararar bakin haure da fataucin kananan yara da ma miyagun kwayoyi a kasar.
Dr. Sulaiman Braimah, daraktan cibiyar da ke ba kasashen Afrika ta yamma shawara game da tsare-tsare masu nasaba da tsaro da ake kira West Africa Centre for Counter Extremism, ya ce sun fara ganin kokarin da kasashen yamma ke yi wajen magance matsalolin da ke addabar kasashen da ke dab da teku.
Wannan tallafin da tarayar Turai ta ba kungiyoyin ya tabbatar da cewa a shirye take ta yaki rashin tsaro a iyakokin kashen da ke dab da teku musamman Ghana, a cewarsa.
Shi kuwa tsohon jami'in diflomasiyya kuma limamin dakarun soja a Ghana mai ritaya Umar Sanda, cewa ya yi aikin tsaro ba na kungiyoyi masu zaman kansa ne kadai ba, kamata ya yi a karfafa sojoji da ‘yan sanda tare da jami’an hukumar shige da fice muddan ana son a kare iyakokin kasar
Ghana ta shiga cikin jerin kasashen da ke fama da matsalar kwararar bakin haure da fataucin kananan yara, da kuma shigar miyagun kwayoyi kasar sakamakon bullar annobar COVID-19, abinda masharhanta ke hasashen zai iya bai wa ‘yan ta'adda damar shigowa kasar musamman a wannan lokaci da suka fara tunkarar kasashen da ke dab da teku.
Saurari cikakken rahoton Hamza Adam daga Kumasi, Ghana
Your browser doesn’t support HTML5