Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ghana Za Ta Zuba Jarin Dala Miliyan 10 Don Kara Bunkasa Masana’antar Yawon Bude Ido


Shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo
Shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo

Masana’antar yawon bude ido ta Ghana da ke farfadowa daga annobar Covid-19, ta sami habaka yayin da gwamnati ta ware dala miliyan $10 don gyara wasu wuraren tarihi da gina sabbin wuraren yawon bude ido a cikin kasar.

Shugaban kasa Nana Akufo-Addo ne ya bayyana hakan a wajen bukin kaddamar da gidan tarihi na kasa da aka yi wa kwaskwarima zuwa na zamani, a babban birnin Accra.

"Gwamnati ta sadaukar da dalar Amurka miliyan 10 don gyarawa da gina wuraren shakatawa da dama da suka hada da wurin shakatawa na tunawa da Kwame Nkrumah, sansanin ajiye bayi na Elmina dake Cape Coast, gidan ajiye kayan tarihi na fadar Manhyia, gidan tarihi na fadar Gbewaa, da fadar Yaa Asantewaa, da sauransu."

Yawon bude ido wata muhimmiyar hanya ce da ke habbaka tattalin arzikin Ghana. Tana samar da kudaden musanya na kasashen waje, da samar da ayyukan yi da wadata ‘yan kasa, tare da karfafa sauran bangarorin tattalin arziki. Sabili da haka, shugaba Akufo-Addo ya kara da cewa, gwamnati ta yi yunkurin kirkiro hanyoyin shawo hankalin masu yawon bude ido zuwa Ghana.

“Wadannan yunkurin sun hada da kara kwarin gwiwar yawon buɗe ido na cikin gida da shirin ‘Mu nufi Ghana’ a Burtaniya”, domin ƙarfafa yawon buɗe ido daga Turai tare da zamanantar da wuraren tarihi da ajiye kayayyakin al’adun gargajiya.

Ma'aikatar yawon bude ido, fasaha da al'adu ta Ghana, ta yi hasashen za a samu kimanin mutane miliyan daya da za su shigo Ghana domin yawon bude ido a wannan shekarar ta 2022. Wadda ya sa take tsammanin kudaden shiga kimanin dala biliyan $2.3

Masanin tattalin arziki, Sarki Imrana Hashiru Dikeni, ya jaddada muhimmancin wannan masana’anta ga tattalin arzikin Ghana inda ya nuna cewa, duk da cewa yawon bude ido na habbaka tattalin arziki, Ghana ba ta baiwa masana’antar muhimmanci.

Sarki Imrana ya jaddada hanyar da habbaka masana’antar bude ido zai karfafa wasu bangarorin tattalin arziki da suka hada da otel-otel da masu dafa abinci.

Saurari cikakken rahoton Idris Abdullah Bako cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG