An yi wani taro biyo bayan harin da aka kai a filin jirgin saman birnin Brussels, inda ministocin shari’a da na harkokin cikin gidan kasashen Tarayyar Turai suna shan alwashin yaki da ta’addanci ta hanyar hadakar bayanan fasinjojin jiragen sama don yakar ta’addanci.
Harin da aka kai kwanakin 3 da suka wuce ya hallaka mutane fiye da 30 ya kuma jikkata sama da 260 a filin jirgin. Ministan harkokin cikin gida na Netherland Ronald Plasterk ya bayyana cewa, kowa ya yarda harin na Brussels ya shafi duk kasashen Turai.
Wannan taron ya wakana a lokacin da hukumomin tsaron Belgium ke ci gaba da fuskantar caccaka game da sakaci da aikinsu na tsaron kasa. Tare da bayyana hujjojin da ke alakanta harin shekaran jiyan da wanda aka kai a watan Nuwambar bara a birnin Paris.
Kwamishinan cibiyar harkokin cikin gidan Turai Dimitris Avramopoulos ma cewa yayi, “wadannan maharani fa girman cikin kasar ne, kuma jami’an tsaro na sane da su. Da ace muna musayar bayanan sirri a tsakanin kasashenmu da ina ganin ba a kai ga haka ba.