Tarar Kotu Ga 'Yan Barandan Siyasa Ya Bayyana Damuwa Kan 'Yancin Kafafen Yada Labarai a Ghana

Tashoshin talabijin Ghana

An yankewa wasu ‘yan barandan siyasa 16 na jam'iyyar NPP mai mulki hukuncin tarar Ghana Cedi 2,400 (wato kimanin $200) ga kowannensu, domin kutsawa da suka yi cikin shirin talabijin da ke gudana kai tsaye.

Lamarin dai ya haifar da cece-kuce a tsakanin ma’aikatan kafafen yada labarai; suna bayyana fargaba game da tsaron lafiyar ‘yan jarida a kasar.

Wata kotun majistare dake Achimota ce ta yanke hukuncin, bayan dukkansu 16 sun amsa laifin da ake tuhumar su da su; hukuncin ya ce idan ba su iya biyan tarar ba, za su kasance a gidan gyaran hali na watanni 3.

Lamarin ya faru ne a yayin wani shirin talabijin na kai tsaye ranar Asabar 7 ga watan Oktoba 2023, inda wasu gungun ‘yan bangan siyasa 16 da ke da alaka da jam’iyyar NPP mai mulki, suka shiga cikin dakin shirye-shiryen gidan telebinjin din UTV dake Accra, babban birnin Ghana, da karfin tsiya, suka ta da hayaniya a cikin shirin dake gudana kai tsaye.

Dalilinsu na kutsen shi ne cewa, wannan shirin ya kasance a kullum ana sukar gwamnati ba bisa ka'ida ba.

Masu ruwa da tsaki a harkokin yada labarai, kamar kungiyar ‘yan jarida ta Ghana (GJA); hukumar yada labaran Ghana; jam’iyar NPP mai ci da babbar jam’iyar adawa ta NDC sun yi Allah wadai da abin da ya faru.

A jawabin da ta faitar ga kafofin labarai, kungiyar GJA ta ce:

"GJA na kira ga gwamnati, kungiyoyi masu zaman kansu (NGOs), kungiyoyin farar hula (CSOs), jami’an diflomasiyya, hukumomin kasa da kasa da dukkan ‘yan Ghana masu kishin kasa da su yi Allah wadai da wannan danyen aiki da wadanda suka kitsa hakan."

Wasu ‘yan jarida sun bayyanawa Muryar Amurka ra’ayinsu game da hakan. Maryam Bawa, ‘yar jarida ce da gidan rediyon Marhaba dake nan Accra.

"Dukkan dan siyasa da zai aika matasa su je su yi ta’asa irin wannan, ya riga ya ajiye kudade a kasa da zai je ya yi belinsu idan an kama su. Gaskiya wannan hukuncin ba wanda ya kamata ba yi bane; hukuncin wanda ya saci dunkulen maggi ne aka yi musu."

AbdulHanan Adam dan jarida ne da gidan telebijin na GHOne, ya ce:

"Rashin jan kunnen wadanda suka aikata makamancin hakan, shi ne ya sa yake kara faruwa. Lokaci ya kai da ya kamata gwamnati ta shimfida wasu matakai da za a magance ire-iren hakan."

Shiko Lauya Anas Mohammed, a nasa bangaren ya ce, ba laifin alkalin da ya yanke hukuncin bane, yanayin karar da hukumar ‘yan sanda suka shigar, shi ne ya yi tasiri wajen hukuncin.

"An shigar da kararsu da laifin, hada baki don aikata laifi da tayar da tarzoma, kuma dukkansu kananan laifuka ne. Amma, hakan na nuni da cewa, idan mutum na da kudi zai iya aikata kowane laifi ke nan. Gaskiya tarar GHC 2,400 ga wannan laifin da suka yi bai baiwa mutane tsoron aikata irin laifin."

Yanzu ya rage ga duk masu ruwa da tsaki, ciki har da jam’iyyun siyasa, su tabbatar da kyakkyawan yanayin da kafafen yada labarai da ‘yan jarida za su rika gudanar da ayyukansu cikin walwala da ’yanci.

Saurari rahoton Idriss Abdallah:

Your browser doesn’t support HTML5

Tarar Kotu Ga 'Yan Barandan Siyasa Ya Bayyana Damuwa Kan 'Yancin Kafafen Yada Labarai a Ghana