Rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin ta bakin kakakin ta SP Usman Abdullahi Jada, wanda ya kara da cewa yanzu haka an dawo da doka da oda a yankin da abin ya faru.
Da yake zantawa da Sashen Hausa, kwamandan 'yan bangar Tiggi ya ce sun kashe 'yan bindiga sama da talatin, amma su ma sun sami asarar jami’ansu 15.
Shugaban kwamitin samar da zaman lafiya na yankin Bali da Gasol, Zubairu Sajo, ya yi kira ga gwamnatin jiha da ta kai musu agajin gaggawa a yankin baki daya.
Ardo Tim Tim wanda ya yi rashin 'yan uwa sakamakon wannan hari ya nuna rashiN jin dadinsa sakamakon ga asarar rayuka da suka yi, tare da kira ga gwamnatin tarayya da ta jiha da su kai musu dauki.
Domin Karin bayani saurari rahotan Lado Salisu Garba.
Your browser doesn’t support HTML5