Taraba: APC Ta Kai PDP Kara

'Yar takarar mukamin jahar Taraba a karkashin inuwar jam'iyar APC, Hajiya Ai'sha Jummai Alhassan

Jam'iyar adawa ta APC a jahar Taraba na kalubalantar jam'iya mai mulki ta PDP bisa zargin nadin shugabanin rikon kwarya a kananan hukumomin jahar.

Jam’iyar adawa ta APC ta jihar Taraba ta shigar da kara a kotu domin kalubalantar rusa majalisun kananan hukumomi tare da nada kantomomi da gwamnatin jahar ta yi.

A cewar jami’yar ta APC, wannan wani yunkuri ne na yiwa dimokradiyya zagon kasa, lamarin da gwamnatin jahar ta musanta.

“Mun garzaya zuwa kotu muna nema a rusa wadannan nade-naden da aka yi na kananan hukumomi na shugabannin riko domin ba daidai ba ne, saboda ya sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya.” In ji shugaban jam’iyar APC a jahar Taraba, Alhaji Hassan Jika Hardo.

A cewar Alhaji Hardo, kamata ya yi zababbun shugabannin kananan hukumomi su mika mulki ga sabbin zababbun shugabanni.

Sai dai Jami’in hulda da jama’a kuma kakakin gwamnatin ta Darius Ishaku Dickson, Alhaji Hassan Mijinyawa, ya ce kuskure ne a aibinta ta domin ba gwamnatin gwamna Darius ba ce ta yi nadin.

“Ba gwamnatin Darius ba ce ta nada shugabannin kananan hukumomi, gwamnatin da ta shude ne ta Dan Baba Suntai.” In ji Alhaji Mijinyawa.

Jam'iyar PDP ce dai ke mulki a jahar ta Taraba bayan Dickson ya ka da 'yar takarar APC.

Domin ji cikakken rahoton, ga wakilin Muryar Amurka Sanusi Adamu da karin bayani:

Your browser doesn’t support HTML5

Taraba: APC Ta Kai PDP Kara – 2:51”