Tanka shake da man petur ta kama da wuta ta kone kurmus a yammacin laraba 16 ga watan nan na nuwamba a kan titin Adetokunbo Ademola da ke unguwar Wuse 2 a Abuja.
Jami'an kashe gobara sun yi nasarar kashe wutar da zuwa hada wannan labari ba a fayyace makasudin gobarar ko adadain asarar da ta haifar ba.
Motar dai ta kama da wuta ne a yayin da al'ummar Abuja ke murmurewa daga zullumin da su ka shiga a makon jiya na yiwuwar kai hare-haren boma-bomai a manyan otal din birnin guda 3.
Baya ga ma irin wannan gobara kusan kullum a kan samu hadurran motoci a titunan Abuja sakamakon tukin ganganci ko kuma al'adar wassu direbobi da kan hau titi bayan sun sha barasa musamman a ranakun karshern mako.
A tsakiyar wannan shekara ma fiye da mutum 30 su ka rasa rayukan su yayin da wata babbar motar daukar kaya ta sullubo daga cikin birnin Abuja ta markade motoci da mutane kan hanyar Mararraba da ta hade birnin tarayyar da jihar Nassarawa; kuma itace babbar hanyar da matafiya ke bi don nufar jihohin arewa maso gabas ta bin tsakaiyar jihar Plateau.