Tankaden PDP: Bamanga Tukur Ya Ce Ya Na Nan Daram

  • Ibrahim Garba

Wani taron jam'iyyar PDP mai mulki a Nijeriya.

Shugaban jam'iyyar PDP mai mulkin Nijeriya, Alhaji Bamanga Tukur ya ce shi fa baya cikin mutanen da tankade da rairayar PDP za su shafa.
Shugaban jam'iyyar PDP mai mulkin Nijeriya, Alhaji Bamanga Tukur ya ce shi zai cigaba da jan ragamar jam'iyyar PDP mai mulkin Nijeriya har bayan tankade da rairayar da ake kan yi a jam'iyyar saboda ba ya cikin wadanda za a kawar.

Da ya ke wa wakilinmu a Abuja, Nasiru Adamu Elhekaya bayani bayan wani taro a Fadar Shugaban Nijeriya na tantance wadanda za a saukar, Bamanga Tukur ya ce ya na nan daram kuma ba zai yi murabus ba. Hatta Jami'in Yada Labaran jam'iyyar Olisa Metuh, wanda shi ma na cikin wadanda aka saukar din, ya ce mutane takwas ne abin ya shafa. Amma da Shugaban Jam'iyya da Sakataren Kudi da Mai Binciken Kudi ba su cikin masu sauka.

Haka zalika, wani mamban kwamitin zartaswar jam'iyyar, Yariman Muri ya ce Alhaji Bamanga Tukur bai yi wani laifin da ya cancanci sauka ba. To saidai kuma wani masanin kimiyyar siyasa mai suna Buhari Bello ya ce Alhaji Bamanga Tukur na da matsala saboda ya mai da kansa dan amshin shatar Shugaba Goodluck Jonathan a maimakon ya dau kowane dan PDP a matsayin nasa.

Your browser doesn’t support HTML5

Tankaden PDP: Bamanga Tukur Ya Ce Ya Na Nan Daram - 2:00