Bisa ga dukan alamu tsuguni bata kare ba a yunkurin hada kan jam’iyun hamayya da nufin kwace iko daga hannun jam’iyar PDP mai mulki a Najeriya.
Wannan ya biyo bayan wani sabani da aka samu tsakanin ‘ya’yan jam’iyar CPC ta jihar Kaduna da shugabannin kungiyar na kasa yayinda hadakar jam’iyar hamayyar ta dauki matakan yin rajista a hukuma zabe.
Jam’iyar CPC a jihar Kaduna tayi zargin cewa, ta gano wadansu masu yunkurin yi mata zagon kasa a wannan hadakar.
Da yake jawabi ga manema labarai a jihar Kaduna, shugaban marasa rinjaye na majalisar dokokin jihar Shehu Usman Adamu Danfulani, yace irin ikirarin da wadansu ke yi na zama shugabannin jam’iyar da ba a ma riga an yiwa rajista ba tukuna, ya sa kwamitin dattijan jam’iyar CPC ta jihar Kaduna, ya kafa wani kwamiti da nufin tsarkake jam’iyar daga dukan matsala.
Wakilinmu Isah Lawal Ikara ya aiko mana da hirarsu da bangarorin biyu.