WASHINGTON, DC —
A yayin da Gwamnan jihar Taraba Danbaba Danfulani Suntai ke cigaba da jinya a Amurka sanadiyyar raunukan da ya samu a wani hadarin jirgin sama, mutanen jiharsa na cigaba da gardandami kan makomarsa. Kuma a yanzu haka akwai shari'o'i a kotuna akalla uku dangane da wannan batu, a cewar wakilinmu na Adamawa Ibrahim Abdul'aziz.
Mutawallen Lau Malam Barau Bante Nyako, ya ce ya kamata a jira har sai gwamnan ya sami sauki ko kuma wata makoma dabam ta kasance. Ya ce haka doka ta tanada. To amma Honourable Silas Jastaf ya ce ba fa yadda za a cigaba da zama haka na tsawon lokaci babu gwamna a jihar.
Haka zalika, wani lauya mai suna Barrister Mustafa Bello ya ce ga dukkannin alamu akwai rashin gaskiya cikin wannan al'amari. Ya ce kotu ce ya kamata ta warware batun saboda jam'iyyar ta shiga rikici.