Masana sun ja kunnen mutane cewa za'a yi ambaliyar ruwa wannan shekarar fiye da shekarar da suka wuce.
WASHINGTON, DC —
Rahotanni da muka samu sun ce a cikin makwanni uku an samu ambaliyar ruwa a kowane sassa na jihohin Kano da Jigawa kamar yadda hukumar dake kula da yanayi ta Nijeriya ta riga ta fada.
Dangane da irin tallafin da gwamnati ke bayarwa Alhaji Awwalu Mohammed Harbo kwamishanan na musamman a jihar Jigawa ya ce lokacin da abun ya faru gwamnan jihar ya kafa kwamitin tantance irin iskilar da jama'a suka fada ciki. Bayan sun ziyarci wurare kamar su Babura da Tankarkar gwamnan ya sake kafa kwamitin tallafawa. Haka ma a jihar Kano tana nata kokarin kaiwa mutanenta da ambaliyar ruwan ya shafa tallafi. Sakataren hukumar kai dokin gaggawa Alhaji Bashir ya ce kwamitin da gwamnan jihar ya kafa ya yi kiyasin gidaje 618 suka rushe kana asarar da aka yi ta kai ta nera miliyan 185. Duk wadannan an tura ma gwamna domin ya san irin taimakon da za'a ba mutanen da abun ya ritsa dasu.
Kafin a kai ga ambaliyar ruwan gwamnatin jihar Jigawa ta dauki wasu matakai inji ta bakin kwamishanan aiki na musaman Awwalu Harbo. Ya ce kafin a fara ruwan sama sun zauna da kananan hukumomi sun umurcesu su tabbatar cewa duk magudanan ruwa ba'a toshesu ba. Haka ma mutane su kiyaye toshe wurare da kasar da suke gini da ita akarkara. Haka ma batun yake a jihar Kano inda aka kafa kwamiti na musamman domin wayar da kawunan jama'a.
Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5