Kama daga dauke harajin shekara guda ganin halin da ‘yan Najeriya ke shiga na tsadar farashin tikitin tafiya kasashen waje.
Babban Daraktan hukumar kula da kungiyoyin fararen hula ta Najeriya wato NCSCN, Blessing Akinlosotu, ya ce kasa da mako guda da kamfanin jirgin saman jigilar fasinjoji na Air Peace ya shiga babin tafiya Landan daga Legas a kan Naira miliyan daya da doriya, kamfanin jirgin saman Birtaniyya da ke tafiya a kan wannan hanyar ya rage farashinsa daga Naira miliyan 3 zuwa kasa da Naira miliyan daya cikin kwanaki 3 kacal lamarin da kungiyoyin ke gani a matsayin yiwa Airpeace zagon kasa.
Ganin yadda fara jigilar fasinjoji zuwa Ingila na kamfanin Airpeace ya fara yin tasiri ga rage farashin tikitin wasu kamfanonin jiragen saman kasashen waje, baya ga ci gaba da farfadowar darajar Naira ga kuma batun fara sayar da man jirgin sama da matatar man kamfanin Dangote ke yi a yanzu, yasa muka tuntubi wasu ‘yan Najeriya ko wadannan matakan sun kawo sauki ga farashin tikitin zirga zirga a cikin kasar kuma akasarin wadanda muka tuntuba suka ce ba wannan maganar.
Kungiyoyin fararen hula dai sun yi kira ga gwamnati da ta ba wa kamfanin Airpeace kariya, dauke masa harajin shekara 1 la’akari da rangwamin farashin da ‘yan kasashen waje ke cin moriya a nasu kasashen kamar yadda darakta a kungiyar NCSCN, Alhaji Gambo Haruna Jagindi ya bayyana.
A wani bangare kuwa, masanin tattalin arziki, Mallam Kasim Garba Kurfi ya ce kamata ya yi gwamnatin Najeriya ta duba ta taimakawa kamfanonin jiragen saman kasa dake zirga-zirga zuwa kasashen waje wanda zai taimakawa kasar samun kudadden shiga.
Duk kokarin ji ta bakin gwamnatin tarayya ta bangaren ma’aikatar kula da sufurin jiragen sama a kan yiyuwar daukewa kamfanin Airpeace haraji na tsawon shekara guda ta kiran wayar tarho da sakon karta kwana ya ci tura a yayin hada wannan rahoton.
An dade ana kai ruwa rana tsakanin kamfanonin jiragen saman kasashen waje da na cikin gida Najeriya a kan gogayya ta fuskar rage farashi da zarar kasar ta dan yunkuro saboda haka kamata ya yi gwamnati ta dage a wannan karon ganin ba a ture Airpeace daga kasuwancin jigila ba in ji masana.
Sauarare rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5