Talauci Zai Ragu Idan Attajirai Suna Bada Zakka- Sheikh Nasir Abdulmuhyi

Wani yana raba ruwan lemo a wajen bude baki.

Yayinda masu ayyukan ibada suke yunkurin neman lada. Wadansu sukan yi amfani da wannan dama wajen neman tallafi domin biyan bukatunsu na yau da kullum.
Yayinda masu ayyukan ibada suke kara yunkurin neman lada. Wadansu sukan yi amfani da wannan dama wajen neman tallafi domin biyan bukatunsu na yau da kullum.

Dalili ke nan da yasa ake tarar da mabarata dukan wuni a kewayen masallatai wadanda ke neman masu hali-baiwa su basu sadaka domin biyan bukatunsu kama daga abin masarufi, ko biyan kudin magani, har a wadansu lotukan wadansu sukan nemi sadakar kudi domin suje su biya kudin haya.

Wakilin Sashen Hausa Nasiru Adamu el-Hikaya ya laburta mana cewa, a cikin hudubarshi, a wani masallaci dake Maitama a birnin tarayya Abuja, Sheikh Nasir Abdulmuhyi yace da dukan attajirai zasu bada zakka kamar yadda Allah ya bukace su suyi, da ba za a rika kukan talauci ba.

Your browser doesn’t support HTML5

Masu Ibada Da Mabarata a lokacin azumi - 3:03