Kungiyar ta kai ziyarar ne karkashin jagorancin lauya mai zaman kanshi Solomon Dalong da nufin kara karfafa dankon zumunci tsakanin Kirista da Musulmi da kuma yarda da juna.
Da yake hira da manema labarai yayin ziyarar, Solomon Dalong ya bayyana cewa, bude baki da ake yi tsakanin mabiya addinan biyu a garuruwa dabam dabam na kasar alama ce cewa, an fara samun zaman lafiya, ya kuma yi kira da a ci gaba da daukar matakan cudanya da fahimtar juna.