Kungiyar NSRP ta hukumar raya kasashe masu tasowa ta kasar Burtaniya da hadin gwiwar cibiyar nazari da bincike kan al’amuran jinsi ta Jami’ar Bayero da kuma takwararta mai bincike da bada horo kan harkokin demokaraddiyya ta gidan Mambayya a birnin Kano ne suka shirya taron.
Masana a fannoni daban daban musamman lamuran da suka shafi rayuwar mata da yara wadanda suka fito daga hukumomin gwamnati da cibiyoyin nazari da bincike, harma da kungiyoyin kare rajin mata da yara da kuma kafofin yada labarai ne suka halarci taron, inda akayi musayar ra’ayi da fahimtar al’amura.
Mallam Aminu Buba dake zaman babban manajan kungiyar NSRP mai kula da shiyyar Arewa maso Yammacin Najeriya, kasancewar take hakkin mata da yara yayi zama ruwan dare a duniya, hakan ne yasa suka shirya wannan taron domin ganin an datse tauye hakkokin mata da yara a jihar Kano.
A yayin taron an kafa kwamitoci da suka yi nazari kan fannonin cin zarafin mata da yara. Bayan nazari da musayar ilimi tsakanin masanan, za a samar da wani daftari da zai zama jagora ga gwamnatoci da hukumomi da kuma kungiyoyin habaka rayuwar mata da yara.
Saurari cikakken rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.
Your browser doesn’t support HTML5