Onarebul Ibrahim Aliyu Solo sakataren jam'iyyar reshen Kaduna yace sun kai kara ne domin tilastawa gwamnatin jihar gudanar da zabukan domin taimakawa al'umma.
Yace gwamnatin jihar Kaduna ta cika yaudara, musamman gwamnan jihar. Lokacin da yake neman zabe yace da an zabeshi cikin wata ukku zai gudanar da zaben kananan hukumomi. Amma bayan zabenshi sai ya nada kantomomi ya basu wa'adin wata ukku. Da wa'adin ya kare ya tsawaita wa'adinsu zuwa wata shida. Da nasu wa'adin ya kare ya nada wasu na wata shida . Yanzu kuma an nada wasu na wani wata shidan.
Mr. Solo yace ana zaluntar kananan hukumomi shi ya sa aka ki gudanar da zabukan saboda tunda aka zabi gwamnatin jihar ko kwandala gwamnatin jihar bata sakar masu ba cikin kudadensu. Bugu da kari kudaden haraji da wasu da ake tarawa daga kananan hukumomi suna shiga aljihun gwamnatin jiha ne.
PDP na bukatar kotu ta ki amincewa da nadin kantomomin da gwamnan yayi. A tilasta mashi ya gudanar da zaben kananan hukumomi.
Saidai jam'iyyar APC mai mulki tace kokari gwamnatin jihar keyi na ganin an gudanar da ingantaccen zabe.
Ga rahoton Isa Lawal Ikara da karin bayani.